Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, ya buƙaci coci-coci su riƙa ƙalubalantar gazawar gwamnati tare da kare ’yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya zargi wasu magoya bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da nuna fushi kan rabuwa ta siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sukayi da ADC.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/shehu-sani-ya-…
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta buƙaci shugaban gasar La Liga ta Spain, Javier Tebas, da ya yi murabus nan take daga mukaminsa, bayan ya kwatanta dabarun yaɗa saƙonnin ƙungiyar da hanyoyin farfagandar gwamnatin Nazi ta Jamus.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/real-madrid-ta…
Shahararren mawakin Najeriya, Davido, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba, duk da cewa kawunsa, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/davido-ya-bayy…
Titi Atiku Abubakar, matar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ta yi gargaɗi kan matsalar safarar mutane, tana mai cewa ’yan matan Najeriya na zama abin damuwa a ƙasashen waje.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/titi-atiku-ta-…
A ranar Alhamis ne Elon Musk ya nuna sabuwar motar Tesla Roadster a wani wurin gwaji na kamfanin SpaceX da ke jihar Texas ta Amurka, yana mai cewa motar za ta iya tashi sama.
Dakarun sojojin Najeriya sun hallaka wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne guda biyu, tare da kwato bindigogin AK-47 guda huɗu yayin wani samame da suka gudanar a Jihar Sokoto.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/sojoji-sun-hal…
Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Abayomi Oyebanji, ya kama wa’adin mulkinsa na biyu bayan rantsar da shi a matsayin gwamna na shida a tarihin jihar.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/an-rantsar-da-…
Masana kiwon dabbobi a jihar Bauchi sun gargaɗi masu kiwo kan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) ba bisa ƙa’ida ba wajen kula da dabbobi, suna mai cewa hakan na iya jawo barazana ga lafiyar dabbobi da mutane.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/amfani-da-magu…
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin wata mata mai suna Maimuna da raunata mijinta, Haruna Ishaka, har ya mutu a ƙauyen Maigoje, da ke gundumar Mai Idanu, ƙaramar hukumar Gashaka ta jihar.
Domin karin bayani 👉explorerhausa.com/yan-sandan-tar…
Daruruwan magoya bayan ƙungiyar Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a a ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke Kano, domin nuna adawa da cire sunan ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC daga jerin sunayen ’yan takarar da hukumar ta fitar.
Karin bayani👉explorerhausa.com/yan-kwankwasiy…
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Karin bayani👉explorerhausa.com/tinubu-ya-na%c…
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar mayar da Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna (Federal Polytechnic, Kaduna) zuwa Jami’ar Fasaha da Nazarin Sana’o’i ta Tarayya (Federal University of Technology and Vocational Studies), Kaduna.
Karin bayani👉explorerhausa.com/tinubu-ya-sany…
Shugaban Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihohi 12 kafin zaɓen 2027, inda za a fara da jihar Kaduna a ranar 24 ga Oktoba.
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta buƙaci Gwamnatin kasar ta fara shirye-shiryen tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Oktoba na 2026, maimakon jiran watan Yunin 2027 kamar yadda gwamnati ta bayyana.
Jihohi huɗu sun amince da kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da zai ba da damar kafa rundunar ’yan sandan jihohi.
Karin bayani👉🔗 explorerhausa.com/jihohi-hudu-su…
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da kashe wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu bisa zargin aikata lalata a cikin wani masallaci da ke birnin Makka.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta bayyana sunayen waɗanda aka kashe, Nazrul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar.
A yau, Juma’a, 16 ga Oktoba, ake bikin ranar abinci ta duniya, wadda ke jaddada muhimmancin inganta hanyoyin samar da abinci da kuma kiyaye dabarun gargajiya da ke ƙarfafa tsarin abinci.
Karin bayani👉explorerhausa.com/remi-tinubu-ta…
325 Followers 2K FollowingSabiu Mustapha is a seasoned journalist and museum professional in Nigeria, boasting an impressive background in both media and museums.
1.7M Followers 21 FollowingThe official Twitter page of the Central Bank of Nigeria. We ensure price and financial system stability and promote sustainable economic development.
245K Followers 139 FollowingThe foremost Anti-Corruption Commission with the mandate of fighting corruption in Nigeria through lawful enforcement and preventive measures. [email protected]
5.4M Followers 209 FollowingFormer Vice President of Nigeria. Waziri Adamawa, Businessman, Father and Philanthropist. ADC Presidential Candidate, 2027.
60K Followers 142 FollowingExecutive Governor of Adamawa State. Businessman, husband and a proud father. Tweets by me are signed AUF and are solely my views.
Retweet not an endorsement
1.3M Followers 1K FollowingThis is the Official Twitter Handle of our great Party, the PDP. Please interact with us our esteemed members, supporters & the general public.
139K Followers 190 FollowingOfficial account of the National Agency for Food and Drug Administration and Control, Nigeria. Follow for updates on the Agency's activities.
769 Followers 29 FollowingWelcome to the Official X Page of the Kogi State Government your go-to source for updates, initiatives, and key developments.